SHUGABAN NAGERIA BULA AHMED TUNUBU ZAI BA MANOMA TALLAFIN KUDI

Shugaba Tinubu Zai ba manoma Yan Nigeria tallafin kudi..

Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya ayyana dokar ta-ɓaci kan batun samar da abinci a ƙasar.

Mai magana da yawun shugaban ƙasar Dele Alake, ne ya bayyana haka ga manema labarai a fadar gwamnatin ƙasar da ke Abuja.

Shugaban ƙasar ya bayar da umarnin mayar da duka al'amuran da suka shafi samar da abinci da ruwan sha, a matsayin manyan abubuwan dogaron rayuwa zuwa ƙarƙashin kulawar majalisar tsaro ta ƙasa.

Alake ya ce umarnin na cikin tsare-tsaren gwamnatin Tinubu na tabbatar da tallafa wa masu ƙaramin ƙarfi a ƙasar.

Ya ce Shugaban ya damu kan yadda farashin kayan abinci ke ƙaruwa da yadda hakan ke shafar talakawan ƙasar.

Shugaban ya kuma bayar da umarnin gaggauta bai wa manoman ƙasar taki da irin shuka domin rage musu raɗadin cire tallafin man fetur.

Ya ƙara da cewa “Dole hukumomin ayyukan gona da ta ruwan sha su yi aiki tare domin tabbatar da ingantuwar noman rani a ƙasar don tabbatar da samar wadataccen abinci a ƙasar a kowanne yanayin shekara

Comments

Popular posts from this blog

WADANDA SUKA SAMU $67 A AVACOIN.....Aiki sukayi tukuru wajen neman referral tare da maida hankali wajen danna maballin Mining, kaima idan ka dage da neman referral kafin sati maizuwa zaka iya tara 400k points da zaka canzasu zuwa $67....Tunda ba kudi ake sakawa ba, banga dalilin da zai hana neman referral a shafinka na Facebook da Status dinka na WhatsApp dama duk inda kasan zaka iya samo referral, abokanka da yan'uwanka masu wayoyi duk zaka iya fahimtar dasu alfanun da ke samu idan aka yi aiki kaga sai kayi amfani da referral dinka wajen shigo dasu, sannan ka nusar dasu cewa baa saka ko sisi a Mining din Avacoin....Kunga ni dai nima yanzu haka referral nake nema ga link dina nan idan baka fara baAkwai tarin alheri a tattare da Magirbi...