Kyari ya maye gurbin Abdullahi Adamu a matsayin shugaban APC


Shugaban jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya, Sanata Abdullahi Adamu ya ajiye mukaminsa bayan kwashe shekara daya da 'yan watanni yana jagorantar jam'iyyar.

Sabon shugaban riƙo na jam'iyyar, Sanata Abubakar Kyari ne ya tabbabar da murabus din Adamu kwana guda bayan kafafen yada labarai a Najeriya sun wallafa rahotanni cewa rashin jituwa tsakanin shugaban na APC da gwamnatin Bola Tinubu ne ya tursasa masa sauka daga kujerar.

Kwamitin gudanarwa na APC din a zamansa na ranar Litinin ya kuma amince da naɗa Sanata Abubakar Kyari wanda shi ne mataimakin shugaban jam'iyyar a ɓangare arewacin Najeriya a matsayin sabon shugaban riƙo na jam'iyyar.

A watan Maris ɗin 2022 ne aka zaɓi Abdullahi Adamu a matsayin shugaban jam'iyyar APC na ƙasa bayan gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni ya yi shugaban riƙo na kusan shekaru biyu.

'Takun-saka da Tinubu'

A watan Yunin 2022, ana jajibarin zaɓen fitar da gwani na ɗan takarar shugaban ƙasa na APC, Sanata Abdullahi Adamu ya sanar da cewa sun yanke shawarar goyon bayan Sanata Ahmed Lawan a matsayin wanda zai riƙe tutar APC a zaɓen 2023 kuma shi ne zai kasance ɗan takarar maslaha.

Lamarin ya tayar da ƙura a tsakanin ƴan siyasa inda waɗansu da dama suka nuna cewa bayan shugabancin Buhari na shekara takwas ya kamata mulki ya koma kudancin Najeriya.

Daga bisani tsohon gwamnan jihar Lagos, Bola Ahmed Tinubu ne ya lashe zaben fitar da gwanin kuma ya zama dan takarar APC a zaben da aka yi a farkon wannan shekarar.

Tinubu ya sha rantsuwar kama aiki a matsayin shugaban Najeriya a karshen watan Mayu.

Tun daga lokacin ne rahotanni ke cewa ana zaman doya da manja tsakanin Shugaban jam'iyyar APC na kasa, Abdullahi Adamu da kuma fadar shugaban kasa, kuma hakan bai rasa nasaba da abin da ya sa Adamun ya yar da ƙwallon mangwaro ya huta da kuda.

Ko a farkon wannan watan ma, Sanata Abdullahi Adamu ya yi ɓaɓatu game da cikon shugabannin da aka sanar na majalissun dokokin kasar, inda ya nuna rashin gamsuwa da zaɓen da aka yi na masu rinjaye da mai tsawatarwa da wadansu mukaman wadanda ya ce ba a tuntuɓe su ba kafin yanke shawara.

Comments

Popular posts from this blog

WADANDA SUKA SAMU $67 A AVACOIN.....Aiki sukayi tukuru wajen neman referral tare da maida hankali wajen danna maballin Mining, kaima idan ka dage da neman referral kafin sati maizuwa zaka iya tara 400k points da zaka canzasu zuwa $67....Tunda ba kudi ake sakawa ba, banga dalilin da zai hana neman referral a shafinka na Facebook da Status dinka na WhatsApp dama duk inda kasan zaka iya samo referral, abokanka da yan'uwanka masu wayoyi duk zaka iya fahimtar dasu alfanun da ke samu idan aka yi aiki kaga sai kayi amfani da referral dinka wajen shigo dasu, sannan ka nusar dasu cewa baa saka ko sisi a Mining din Avacoin....Kunga ni dai nima yanzu haka referral nake nema ga link dina nan idan baka fara baAkwai tarin alheri a tattare da Magirbi...