NAFDAC ta gargaɗi mutane kan shan lemon kwalba na 'Sprite'
Hukumar tabbatar da ingancin abinci da magunguna ta Najeriya ta ce tana gargaɗin al'ummar ƙasar game da shan lemon kwalba na 'Sprite' bayan da ta gano gurɓataccen irin wannan lemo a kasuwa.
Hukumar ta NAFDAC ta ce ta gano lemon ne bayan binciken da ta yi sanadiyyar koken da ta samu daga wasu masu amfani da lemon.
NAFDAC ta ce binciken nata ya gano kiret biyar na irin wannan lemo a kwalba mai girman 50cl, inda aka ga ɓurɓushin wani abu na yawo a cikin lemon.
Tuni aka tura wannan gurɓataccen lemo zuwa ɗakin bincike na hukumar domin tantancewa.
Haka nan hukumar ta ce ta bayar da umarnin zagayawa domin ƙwato irin waɗannan samfuri na lemon.
Haka nan an buƙaci kamfanin da ke sarrafa wannan lemo da ya dawo da duk irin wannan kwalba da ya sayar, sannan ya kai wa hukumar cikakkun bayanai.
NAFDAC ta kuma buƙaci duk wanda ya sha irin wannan lemo ko ya san wanda ya sha kuma yake jin ba daidai ba game da lafiyarsa, ya nemi agajin likitoci.
Bayanin lemon da aka gano yana ɗauke da ƴan ƙwallon shi ne:
BN:AZ6 22:32
MFD:180423
BB:180424
Comments
Post a Comment